Sharuɗɗan Sirrin EasyShare
Sabunta na ƙarshe: 25 Maris, 2023
%3$s (wanda anan ana nufin "mun", ko "mu") shine mai ba da EasyShare ("Sabis") da ƙungiyar da ke da alhakin bayanan sirri da aka sarrafa dangane da Sabis. Muna kula da sirrin ka kuma muna tunanin yana da mahimmanci ka san dalili da yadda muke sarrafa keɓaɓɓen bayanan ka. A cikin Sharuɗɗan Sirrin EasyShare ("Sharuɗɗan"), saboda haka zamu yi bayani akan abubuwan da ke gaba:
1. Tari da Sarrafawa: wadanne bayanai za mu tattara da yadda muke amfani da su;
2. Ma’ajiya: yadda za mu adana bayananku;
3. Rabawa da Tura: yadda muke raba ko tura bayanan ku;
4. Haƙƙokinku: haƙƙoƙinku da zaɓuɓɓukan ku dangane da tsara bayanan ku;
5. Tuntuɓe Mu: yadda zaku iya tuntuɓar mu da kowace ƙarin tambayoyi.
Da fatan za a karanta waɗannan Sharuɗɗan a hankali kuma ka tabbata ka fahimci ayyukanmu game da keɓaɓɓen bayanan ka kafin ka yarda kuma kafin ka fara amfani da Sabis ɗin. Ba a wajabta muka izinin sarrafa bayananka dangane da Sabis ɗin ba, amma da fatan za ka san waɗannan abubuwan: IDAN BAKA YARDA DA WADANNAN SHARUDU KO KUMA IDAN KA JANYE IZININ KA, BA ZA KA IYA AMFANI DA SABIS DIN BA.
1. Tari da sarrafawa
Bayanai da dalilai
• EasyShare na tsara SMS naku, lambobin waya, kalanda, hotuna, bidiyo, sauti, kida, manhajoji, saituna, rikodin kira, rubuta bayanai, fayiloli ko wasu abubuwan da aka adana a cikin na'urar (a dunƙule, “Abubuwan da ke ciki”) tare da algorithm dake akan na'urarku domin fasalin maballin kunna na’ura na one-touch da dawowa da tanadi. Da fatan za a lura cewa irin waɗannan bayanan sirri za a sarrafa su kawai a cikin na'urar ka kuma ba za a tattara su ba, ba za mu shiga ko loda su zuwa sabobin mu.
• A cikin ƙasashe/yankunan da ake samun aikin asusun wayar hannu, EasyShare tana aiwatar da bayanan asusun wayar hannun ka don manufar nunin bayanan asusun idan ka shiga cikin na'urar.
• EasyShare Shirin Inganta Kwarewar Mai Amfani: Zaku iya zabar shiga cikin Shirin Nishadin mai Anfani na EasyShare a karan-kanku. Ida kun zabi shiga, domin inganta Sabis din mu, zamu tattaro alamar gane wayar ku ko alamar gane manhaja, samfurin na’ura, alamar na’ura, sigar na’ura r Android, sigar manhaja, dabi’ar yanayin anfani a cikin manhajar, (kamar, burauzin, latsawa, da sauran su.) lambar kasa da kuma lambar kus-kure a yayin da fasalin manhajar yaki aiki da kyau da sauran su. Za’a gudanar da irin wadannan ingantattun nazari a matsayin hanyar tattara bayanai ba tare da an gane wata alamar sirri ko dabi’u ba. A kowane lokaci zaku iya zabar kashe maballin ta hanyar shiga zuwa Saituna > Shiga Shirin Nishadin mai Anfani na EasyShare a cikin manhajar EasyShare. Idan kun kashe wannan maballin, zamu dakatar da irin wannan tsara bayanan a cikin Sabis har sai kun sake-amincewa . Da fatar zaku san cewa wannan fasalin kadai za’a same shi ne akan wadansu kebantattun na’urori saboda samfurin na’ura, sigar na’ura ko ka’idodin yanki, dangane da ainihin samuwa. Kadai zamu tsara bayanai ne a kar-kashin wannan bayyanannen fasalin idan kun kunna ko yi anfani da wannan fasalin.
Muna aiwatar da bayanan don dalilai na sama bisa izinin ka ga waɗannan Sharuɗɗan. Duk da haka, a yayin da aka bada dama ta hanyar dokokin da suka dace, wadansu dokokin zasu iya dacewa a wasu kebantattun yanayi kamar yadda a bayyana a cikin Sashe na 2 na Ka’idodin Sirrin mu. Idan kunyi nufain rashin yin anfani da dukkan fasullan sabis din, da fatar zaku janye yarda ku ta hanyar tsarin da aka bayyana a cikin Sashe na 4 na Sharuddan.
Tsaro:
Muna kula da kare bayanan sirrinka. Mun sanya matakan tsaro masu dacewa, gami da shi amma ba'a iyakance ga ɓoyayye da dabarun ɓoye suna ba, waɗanda aka ƙera don kare keɓaɓɓen bayanan ka daga amfani, lalacewa, ko asara ba tare da izini ba. Za mu yi iya ƙoƙarinmu don kare bayanan sirrinka. Idan kana zargin kowane amfani mara izini, lalacewa, ko asarar bayanan keɓaɓɓen ka, da fatan za a sanar da mu nan da nan ta amfani da bayanan tuntuɓar da aka bayyanar da su a ƙasa.
2. Ma’ajiya
Lokaci:
Bayanai masu alaka da asusun shiga waya da Shirin Inganta Nishadin mai Anfani kadai za’a ajiye su ne a cikin sabar mu na tsawon lokacin da ya dace domin tsara bayanai. Don wasu bayanai, musamman abubuwan da kuka yi anfani da Sabis din waje taransifa, kadai za’a tsara su ne a cikin na’urar ku kuma ba za’a kiyaye su ba, ba zamu iya ganin su ba, ko kuma dora su a kan sabar mu. A halin yanzu, za mu riƙe:
• Bayanan sirri masu alaƙa da amfani da haƙƙin jigon bayanai, yarda da bayanan hulɗar abokin ciniki na tsawon shekaru biyar daga hulɗar ka ta ƙarshe da mu;
• Ana sarrafa bayanan adanawa da log ɗin app don dalilai na tsaro fiye da watanni shida daga ranar da aka ƙirƙira su.
Da zarar lokacin riƙewa ya ƙare, za mu share ko ɓoye keɓaɓɓen bayanan ka, sai dai in an buƙaci wasu dokoki da ƙa'idodi.
Wuri:
Don samar da matakan kariya iri ɗaya kamar na ƙasa/yankin mai amfani da kuma amsa buƙatun masu amfani da kyau, wurin da ake adana bayanai ya bambanta ga masu amfani a ƙasashe/yankuna daban-daban. Da fatan za a koma zuwa sashin Ajiya da Canja wurin Ƙasashen waje a cikin Manufar Sirri don gano inda aka adana keɓaɓɓen bayanan ka.
3. Rabawa da Turawa
Dangane da dora bayanai akan saba, mune zamu tsara bayanan ku da kan mu ko ta hanyar anfani da kamfanin da muke da hadin gwiwa ko masu samar da sabis wadanda ke wakiltar mu. Bugu da kari, za mu raba bayanan ka ne kawai lokacin da ake buƙata don amsa wani tsari na doka ko buƙata daga wata hukuma mai ƙarfi bisa ga ƙa'idodin da suka dace.
Tunda muna aiki a matakin kasa-da-kasa,, kuma don ba ku damar amfani da samfuran mu a duk fadin duniya, za’a iya yin taransifar bayanan kun a sirri ko wasu kungiyoyin dake a wadansu kasashe/yankuna na iya anfani dasu ko kuma suyi anfani dasu daga nesa. Muna bin dokoki kan tura bayanan sirri tsakanin ƙasashe don taimakon tabbatar da kare bayanan ka, a duk inda ya kasance.
4. Haƙƙokinku
Kana da haƙƙoƙi daban-daban dangane da bayanan da muke riƙe game da kai.
Janye Izini
Kana iya a kowane lokaci ka zaɓi janye izininka don sarrafa bayananku ta danna maɓallin Janye yarda button, wanda za'a iya samuwa a ƙarƙashin Sirri > Sharuɗɗan Sirri a cikin Profile na Sabis. Idan ka janye izininka, za mu daina sarrafa bayananka a cikin Sabis har sai ka sake yarda da waɗannan Sharuɗɗan.
Sauran Hakkoki:
Don aiwatar da sauran haƙƙoƙinka (kamar gyara, gogewa, ƙuntatawa aiki, ƙin yarda ko ɗaukar bayanai, dangane da madaidaitan dokokin kariyar bayanai), da fatan za a yi amfani da bayanan tuntuɓar da ke ƙasa.
Ƙorafi:
Kana da damar shigar da ƙara zuwa ga hukuma mai kulawa.
5. Tuntuɓe mu
Idan kuna da wasu tambayoyi game da waɗannan Sharuɗɗan ko tsara bayanan ku na sirri, idan kuna buƙatar bayar da rahoton wata matsala ko tuntuɓar Wakilin mu mai samar da Kariya ga Bayanan, ko kuma idan kuna son cin gajiyar haƙƙoƙin ku ƙarƙashin dokokin kariyar bayanai da sirri, da fatar za’a taba. nan don tun-tunbar mu. Za mu nemi magance buƙatarka ba tare da bata lokaci ba, kuma a kowane yanayi a cikin kowane lokaci da aka tanadar don ƙa'idodin kariyar bayanai.
Ana iya sabunta waɗannan Sharuɗɗa daga lokaci zuwa lokaci. Za mu sanar da kai ta hanyar da ta dace na kowane gagarumin canje-canje Duk ayyukan da aka ambata a cikin waɗannan Sharuɗɗan za a yi su daidai da Manufar Sirri , wanda daga ciki zaku iya samun ƙarin cikakka bayanai game da ayyukanmu.